التصنيفات
غير مصنف

Surah Maryam ( Mary ) [16-35]

وَاذْكُرْ فِي الْكِتَابِ مَرْيَمَ إِذِ انتَبَذَتْ مِنْ أَهْلِهَا مَكَانًا شَرْقِيًّا ( 16 ) 

Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen gabas.

فَاتَّخَذَتْ مِن دُونِهِمْ حِجَابًا فَأَرْسَلْنَا إِلَيْهَا رُوحَنَا فَتَمَثَّلَ لَهَا بَشَرًا سَوِيًّا ( 17 ) 

Sa’an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.

قَالَتْ إِنِّي أَعُوذُ بِالرَّحْمَٰنِ مِنكَ إِن كُنتَ تَقِيًّا ( 18 ) 

Ta ce: “Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!”

قَالَ إِنَّمَا أَنَا رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَامًا زَكِيًّا ( 19 ) 

Ya ce: “Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki.”

قَالَتْ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَامٌ وَلَمْ يَمْسَسْنِي بَشَرٌ وَلَمْ أَكُ بَغِيًّا ( 20 ) 

Ta ce: “A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?”

قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٌ ۖ وَلِنَجْعَلَهُ آيَةً لِّلنَّاسِ وَرَحْمَةً مِّنَّا ۚ وَكَانَ أَمْرًا مَّقْضِيًّا ( 21 ) 

Ya ce: “Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata rahama ce daga gare Mu.’ Kuma abin yã kasance wani al’amari hukuntacce.”

فَحَمَلَتْهُ فَانتَبَذَتْ بِهِ مَكَانًا قَصِيًّا ( 22 ) 

Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.

فَأَجَاءَهَا الْمَخَاضُ إِلَىٰ جِذْعِ النَّخْلَةِ قَالَتْ يَا لَيْتَنِي مِتُّ قَبْلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسْيًا مَّنسِيًّا ( 23 ) 

Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta ce “Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta!”

فَنَادَاهَا مِن تَحْتِهَا أَلَّا تَحْزَنِي قَدْ جَعَلَ رَبُّكِ تَحْتَكِ سَرِيًّا ( 24 ) 

Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, “Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.

وَهُزِّي إِلَيْكِ بِجِذْعِ النَّخْلَةِ تُسَاقِطْ عَلَيْكِ رُطَبًا جَنِيًّا ( 25 ) 

“Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon ya zuba a kanki yanã ‘ya’yan dabĩno, ruɗabi nunannu.”

فَكُلِي وَاشْرَبِي وَقَرِّي عَيْنًا ۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ الْبَشَرِ أَحَدًا فَقُولِي إِنِّي نَذَرْتُ لِلرَّحْمَٰنِ صَوْمًا فَلَنْ أُكَلِّمَ الْيَوْمَ إِنسِيًّا ( 26 ) 

“Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, ‘Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba.”

فَأَتَتْ بِهِ قَوْمَهَا تَحْمِلُهُ ۖ قَالُوا يَا مَرْيَمُ لَقَدْ جِئْتِ شَيْئًا فَرِيًّا ( 27 ) 

Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da shi. Suka ce: “Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma!

يَا أُخْتَ هَارُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ امْرَأَ سَوْءٍ وَمَا كَانَتْ أُمُّكِ بَغِيًّا ( 28 ) 

“Yã ‘yar’uwar Hãrũna! Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba.”

فَأَشَارَتْ إِلَيْهِ ۖ قَالُوا كَيْفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي الْمَهْدِ صَبِيًّا ( 29 ) 

Sai ta yi ishãra zuwa gare shi, suka ce: “Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã jãrĩri?”

قَالَ إِنِّي عَبْدُ اللَّهِ آتَانِيَ الْكِتَابَ وَجَعَلَنِي نَبِيًّا ( 30 ) 

Ya ce: “Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi.”

وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَانِي بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ مَا دُمْتُ حَيًّا ( 31 ) 

“Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar inã da rai.”

وَبَرًّا بِوَالِدَتِي وَلَمْ يَجْعَلْنِي جَبَّارًا شَقِيًّا ( 32 ) 

“Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba marashin alhẽri.”

وَالسَّلَامُ عَلَيَّ يَوْمَ وُلِدتُّ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّا ( 33 ) 

“Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai.”

ذَٰلِكَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ ۚ قَوْلَ الْحَقِّ الَّذِي فِيهِ يَمْتَرُونَ ( 34 ) 

Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta.

مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٍ ۖ سُبْحَانَهُ ۚ إِذَا قَضَىٰ أَمْرًا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُ كُن فَيَكُونُ ( 35 ) 

Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Yã hukunta wani al’amari sai kawai Ya ce masa, “Kasance.” Sai ya dinga kasan cẽwa.